Sam Smith da Burna Boy: Abubuwan da suka kamata ku sani kan wakar ‘My Oasis’

Sam Smith da Burna Boy: Abubuwan da suka kamata ku sani kan wakar 'My Oasis'

Sam Smith and Burna Boy

Bayanan hoto,

Sam Smith da Burna Boy

Fitaccen mawakin nan na Ingila Sam Smith ya sanar cewa ranar Alhamis din nan zai fitar da wakarsa mai suna ‘My Oasis’ wadda ya yi tare da mawakin Najeriya Burna Boy.

Shi kuwa Burna Boy, wannan hadin gwiwar na zuwa ne bayan wakar Jerusalema wadda ya yi da Master KG a watan Yuni.

Smith ya wallafa bidiyon kayan kidan da ya yi wakar tare da mawakin na Najeriya a shafinsa na Instagram.

Wannan ce waka ta farko da zai fitar tun watan Afrilu bayan wakarsa da Demi Lovato mai suna ‘I’m Ready’.

Sam Smith ya yi wakoki da dama cikinsu har da ‘Money On My Mind’, ‘Stay with Me’ da kuma ‘Writing’s On the Wall’, wacce ta sanya ya lashe gasar Oscar in 2016.

Ana hasashen cewa mawakin na Birtaniya ya mallaki £33m.

Yadda masu son wakoki suka ji da hadin gwiwa tsakanin Sam Smith da Burna Boy

Magoya baya sun yi ta yaba wa Burna Boy bisa hada gwiwa da ya yi da Sam Smith. Koda yake har yanzu wakar ba ta fita ba, amma tuni suka fara cewa za ta yi dadi.

Mawakin na Birtaniya ya wallafa sakon Twitter da ke cewa “ina matukar kaunar Burna. Za mu kayatar da kowa”.

A martanin da ya yi, Burna ya ce “za mu burge magoya ba ni da kai, Sam.”

Wani mai son wakokin Burna, mai suna The Boogie Man, ya yaba kan yadda ake damawa da gwanin nasa yana mai cewa kowanne mawaki yana son hada gwaiwa da shi.

Skip Twitter post, 2

End of Twitter post, 2

Ba wannan ne karon farko da Burna ya hada gwiwa da mawakan Turai da Amurka ba, domin kuwa a baya ya yi waka tare da Beyonce, Stormzy da kuma Ed sheeran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Michael Jordan

Michael Jordan announces first donations from $100 million pledge

Bobby Wagner: Discipline is going to be biggest thing for players this season

Bobby Wagner: Discipline is going to be biggest thing for players this season